JSC ta dakatar da magatakarda, tare da gargadin wani Alkali a jihar Kano

FB IMG 1760198620995

Hukumar Kula da Ma’aikatan Shari’a ta Jihar Kano (JSC) ta dauki matakai kan wasu jami’anta bayan kammala binciken Kwamitin Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a na Alkalanci (JPCC).

A wata sanarwa da kakakin hukumar, Baba Jibo Ibrahim, ya fitar, JSC ta gargadi Alkalin Kotun Shari’a ta   Dambatta, Umar Bala Musa, bisa jinkirta sakin takardun zaman kotu fiye da wa’adin kwanaki bakwai da doka ta tanada.

Haka kuma, hukumar ta dakatar da babban magatakarda na Kano Multi-Door Courthouse, Saifuddeen Mukhtar Abdullahi, ba tare da albashi ba, saboda binciken ‘yansanda kan zargin karkatar da kudaden zuba jari na ƙungiyar ma’aikata da kuma yin amfani da takardu na bogi.

A wani lamarin daban, JSC ta dakatar da Kamal Ado, jami’in kotun Kurna, ba tare da albashi ba, yayin da yake fuskantar shari’a a babbar kotun tarayya kan zargin hulɗa da miyagun ƙwayoyi, kai hari ga jami’an bincike da lalata hujjoji.

Hukumar ta kuma janye hukuncin da aka yiwa Ibrahim Adamu  na shekaru hudu, bayan ya kammala dakatarwar watanni shida tare da nuna nadama da kyautata halayya.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *