Kano Pillars ta yi Nasarar lashe kofin Shugaban Kasa a Abuja.
PRESIDENTIAL CUP
Best Seller Channel
A yammacin Lahadi ne kungiyar kano pillars ta fafata a wasan karshe na sharar fagen wasannin kaka mai zuwa a garin Abuja.
Akwa United ce ke kan gaba da farkon wasan da ci 1 da nema a minti 23 na farkon wasan.
Daga bisani Kano Pillars ta dawo cikin wasan har sai da dan wasan Pillars Mai suna Kokoette Udo wanda ya maye gurbin Aniekeme Asuquo shi ya bawa kungiyar nasarar zura kwallo mai kyau a ragar Akwa United a minti na 84 na karshen wasan in da ka tashi wasa Akwa 1 1 Pillars.
Best Seller Channel
Wannan kunnen dokin ita ta bawa kungiyar kano Pillars zama zakara a wannan gasar ta Mai girma shugaban Nigeria Malam Muhammadu Buhari da maki 7
Wasan da kano Pillars ta fara bugawa ta yi ne da kungiyar Sunshine, in da Pillars ta lallasata da ci 3 da 1.
Wasa na biyu kano Pillars ta sake karawa da kungiyar Lobi Star, nan ma Pillars ta casa Lobi da ci 2 sa 1.
Best Seller Channel
Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars kwararriyar kungiyar kwallon kafa ce ta Najeriya da ke (Kano. Sai Masu Gida)
Suna wasa a matakin farko a kwallon kafa ta Najeriya, Firimiyar Najeriya.
Suna taka leda ne a Filin wasan su dake kano kofar mata, Sani Abacha Stadium.