Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya bada umarni an kaddamar da wani gagarumin hari mai matukar muni kan ‘yan ta’addan ISIS a jihar Sokoto Nigeria
Trump yace harin ya shafi mafakar kungiyar ISIS ne a jihar Sokoto wadanda suke kai hari da kashe Kiristoci a Nigeria, yace idan ba su daina kisan Kiristocin Nigeria ba, za su fuskanci mummunan sakamako kamar yadda suka fara gani a daren yau
Ya ƙara da cewar wannan hari da Amurka tayi a jihar Sokoto duk duniya Amurka ne kadai ke da karfin iya kaddamar da harin, Kasar Amurka ba za ta bari tsattsauran ra’ayin ta’addancin Musulunci yayi karfi ba a Nigeria
Amurka tayi amfani da sansanin Sojin ruwanta na USS Paul Ignatius dake Rota a Kasar Spain ta harbo hatsabibin makamin Missile mai gudu kamar walkiya mai suna “Tomahawk Missile” zuwa jihar Sokoto.
Sannan a cikin daren Alhamis din ma’aikatar kula da harkokin waje na Nigeria ta fitar da sanarwa jim kadan bayan kaddamar da harin, tace da amincewar Gwamnatin Nigeria aka kaddamar da harin domin a durkukusar da karfin ‘yan ta’adda, kuma an dau matakin da zai kauce taba fararen hula
Sai dai wani abin fashewa da ake zargin yana cikin tarkacen makami mai linzami da Amurka ta harba zuwa Sokoto yayi saukar bazata a garin Jabo karamar hukumar Tambuwal jihar sokoto duk a cikin daren, bayan abin ya fashe mutanen garin sun gudu zuwa neman mafaka
Zuwa yanzu dai ba’a san girman ta’adin da harin Amurka ya yiwa ‘yan ta’adda a Sokoto ba, fatan mu kar a fake da wannan a taba wanda bai ji ba bai gani ba kamar yadda suka saba yi a sauran Kasashen Musulmi
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t