‘Ko Da Tsiya-Tsiya’ Ko Da Tsiya-Tsiya, Ba Na Tunzura Rikici Ba Ne’ Abdullahi Abbas

Alfijr ta rawaito Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya musanta zarge-zargen da ake masa na amfani da kalaman tunzura gangamin yaƙin neman zaɓe a tarukan siyasa.

Kalmar “ko da tsiya ko da tsiya-tsiya, sai mun ci zaɓe”, ba baƙon abu ne domin an sha jiyo Abdullahi Abbas na ambato wadannan kalamai a tarukan siyasa tun daga zaben 2019.

Ƴan adawa a jihar na cewa irin wadannan kalamai na Abdullahi Abbas, wata alama ce da ke nuna cewa mai yiwuwa akwai wani mummunan nufi da APC ta yi game da babban zaɓe da ke tafe a jihar.

Sai dai a tattaunawarsa da BBC, Abdullahi Abbas ya ce an yi wa maganganunsa mummunar fahimta ce kawai.

Da aka ƙara tambaya kan dalilan amfani da wadannan kalamomi da ke kama da na tunziri rikici, sai ya ka da baki ya ce:

“Tsiya-tsiya takobi ce? Tsiya-tsiya mashi ne? Tsiya-tsiya wuƙa ce? Tsiya- tsiya bindiga ce? Ai dagewa ce lallai ka tsaya sai an ci zaɓe, abin da ake nufi kenan.

Abdullahi Abbas ya ce ai “abokan hamayyar mu shaƙiyanci ne, ai sun san abin da muke nufi, batu ne na jefa ƙuri’a kuma mu kuri’a da ake jefawa muke nufi da tsiya-tsiya, domin ita ce tsiyar ai da muke nufin zamu saka musu a zaɓe”.

Shugaban na APC a Kano, ya ce wannan karon zaɓe ne za a yi falan ɗaya, domin a baya an sha su, sun kuma warke, “wai inconclusive bayan su sun san cewa cutarsu aka yi”.

Abbas ya ce yanzu waɗannan kalamai na shi na nufin ba za su sake bari a maimaita hakan ba a zaɓe mai zuwa. “Ba zamu bari a sake cutar mu ba”.

Ana yi wa Abdullahi Abbas laƙabi da “ko da tsiya”

“Ni ba ni da ja da aƙidar dimokuradiya, domin kalmomina ba na husuma ba ne, ina da asali, na fito daga gidan sarauta, ina iya zama sarki, don haka ni ba mutum ba ne da zai so haddasa rikici”.

Abbas dai na nuna cewa kalmominsa hausa ce, kuma dama shi ɗan siyasa duk abin da ya ce sai na sauya ma sa.

A cewarsa siyasar Kano ta gaji haka, “mu ‘yan Kano haka muke siyasarmu, kalmominmu sun sha bamban kuma shi talaka da ake yi domin shi yasan me muke nufi.

Abbas ya tunasar da kan sa cewa ai ya taɓa yin waɗannan kalamai a baya, kuma babu wanda ya tunzura, kuma shi wai bai ce kowa ya ɗau makami ko ya yi fitina ba, kalamominsa na nufi a kasa a tsare kar ayi ma su maguɗi.

“A zaɓen baya mu aka yi wa maguɗi, mu fa mun fi son kowa ya zauna lafiya, kalmomina burga ce ta ‘yan siyasa”.

Da aka yi masa tambaya ko shin ba su da wani abin burga na jan hankali mutune su zaɓe su, sai ya ce, ba wai ba su da ayyukan raya kasa ba ne, kawai dai su hausawa sai da haka.

Ya kuma zargi cewa “ai su masu korafi ai nasu shaƙiyanci da iyayen gidansu ya fi nasu muni”.

Ya ce su ‘yan APC galatsine suke yi amma ga ɓarayin kuri’a wanda kowani talaka da abokin hamayya ya san abin da suke nufi.

Abbas ya ce sun haramta ɗaukan makamai da kalaman tunzuri, domin duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci.

Siyasar ba ta da maraba kamar ta sauran duniya, kawai dai tunda batu ne na harshen hausa dole su yi ta yadda ‘yan jihar Kano hausawa za su fahimce su, in ji Abdullahi Abbas.

BBC Hausa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *