Kotu Ta Daure Abbas Adamu Dake Unguwar Tudun Fulani Kurna Shekaru 14 Bisa Laifin Kisan Kai

Alfijr

Alfijr ta rawaito mai shari’a
Amina Adamu Aliyu dake kotu mai lamba 10 Miller Road a kano, ta daure wani mai suna Abbas Adamu dake unguwar Tudun Rubidi dake Kurna karamar hukumar Dala ta jihar Kano shekaru 14.

An gurfanar da Abbas Adamu mai sha karu 20 a gaban babban kotun, bisa zargin da ‘ba almakashi a kirjin wani Shafiu Umar ranar 1/01/2017 da misalin karfe 10:30 na dare.

Da farko dai Abbas Adamu yaron Kanti ne a unguwar Tudun Rubidi dake Kurna, sai shafi u ya zo kantin nasa bige ya sha abin maye, sai suka fara hayaniya tsakaninsu, daga Karshe dai Abbas ya shiga shagon ya dauko almakashi ya bugawa Shafi u a kirjinsa, wanda wannan yayi Sanadiyyar Mutuwarsa.

Alfijr

Lauyoyin gwamnati sun gabatar da shaidu har guda 5 na tabbatar da wanda ake zargi shi yayi sanadin mutuwarsa.

Bayan da kotu ta bawa lauyan Abbas damar kariya, Abbas yayi bayanan kariya, sannan ubangidansa mai shagon shima ya bada shaidarsu.

Alfijr

Daga Karshe mai shari’a tayi watsi da shaidun wadanda ake tuhuma, ta kuma karbi shaidun lauyoyin gwamnati saboda ingancinsu.

Mai shari’a ta sake tambayar lauyoyin cewar ko an taba samun Abbas da makamancin wannan laifin? Lauyoyin suka tabbatar da ba a taba samunsa ba.

Alfijr

Lauyan Abbas ya roki kotu ta sassauta masa saboda karancin shekaru da kuma wannan shine karonsa na farko, kuma gashi maraya.

Da take karanto hukuncin a ranar Laraba 2/03/2022 mai shari’a Amina Adamu Aliyu take, a ka idar laifin nasa hukuncin kisa ne a kansa, amma sai shari’a ta bamu damar zamu iya sassautawa bisa wasu dalilai.

Alfijr

Sannan idan aka kalli karancin shekarunsa da kuma watakila zai iya amfanawa al umma a nan gaba, don haka wannan kotu ta daure shi shekaru 14 kuma zai fara ne tun daga randa aka kama shi.

Allah ya kiyashemu da hawa dokin zuciya ameen.