Kotu Ta Daure Benzema Dan Wasan Madrid

An samu Benzema da laifin cin amana kan batun da ya shafi wani faifan bidiyon lalata na wani tsohon dan kwallon Faransa da suka taka leda tare 

Kotu ta yanke wa Karim Benzema hukuncin ɗaurin gyara hali na shekara ɗaya tare da umartar ya biya tarar dala 84,000.

Benzema mai shekara 33 yana cikin mutum biyar da aka gurfanar a watan da ya gabata, domin karbar kudi a hannun Mathieu Valbuena da ikirarin zai wallafa bidiyon ga duniya a 2015.

An kori Benzema daga tawagar kasar Faransa kusan shekaru shida.

 A ranar Laraba ne aka samu Karim Benzema da laifin hada baki wajen bata wa tsohon abokin wasan Faransa Mathieu Valbuena suna da  faifan video na fasadi. 

 Wata kotu a Versailles ta sami Benzema, mai shekaru 33, da laifin “dumu dumu” a cikin al’amarin da ‘yan bakar fata suka yi yunkurin karbar kudi daga Valbuena kan wani faifan vedeo. 

An yanke wa dan wasan na Real Madrid hukuncin dakatar da shi na tsawon watanni 12 da kuma tarar Yuro 75,000 Dollars $84,150.

Hukuncin dai shi ne na baya-bayan nan na wata doka da ta samo asali tun shekarar 2015 wadda aka kori Benzema daga tawagar kasar Faransa kusan shekaru shida. 

A ranar Laraba ne lauyoyin Benzema suka shaida wa manema labarai cewa suna da niyyar daukaka kara kan hukuncin. 

Benzema na daya daga cikin mutane biyar da aka gurfana a gaban kotu a watan da ya gabata, kan yunkurin bata sunan wani faifan bidiyo da aka sace daga wayar Valbuena. 

Jaridar Kasar England The Mirror ta rawaito Dan wasan gaba na Faransa bai halarci gwajin kwanaki uku ba,  saboda dalilai yana atisaye tare da Real Madrid gabanin babban wasan La Liga da Barcelona.

Best seller Channel 

Slide Up
x