Kotu Ta Sake Daure Abdullahi Tajuddeen Shekara 5 A Kano

Alfijr

Alfijr ta rawaito, hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, a yau Litinin 28 ga watan Fabrairu, 2022, ta samu hukuncin daurin shekaru 5 a kan wani ma’aikacin ofishin canji, Abdullahi Tajuddeen, a gaban mai shari’a Lawan Wada na babbar kotun jihar Kano.

Alfijr

Tuhume tuhumen da ake wa Abdullahi na da alaka da cin amana.

Hukumar ta gurfanar da shine a gaban kuliya a watan Nuwamba 2015 a kan laifuka biyar da suka hada da cin amana.

Alfijr

Wanda ake kara, a wani lokaci a watan Satumbar 2011, ya umarci wanda yayi kara da ya tura masa dalar Amurka $140,200 (daidai da N22, 109, 540.00) ga daya daga cikin kwastomominsa, Huzhou Fuxing, wanda ke da kamfanin masaka a kasar Sin.

Wanda ake tuhumar ya yi ikirarin cewa an tura kudin zuwa Fuxing ta wani banki a ranar 20 ga Satumba, 2015.

Alfijr

Sai dai, na’urar wayar da aka gabatar a matsayin shaidar, ta kasance ta jabu ce.

Mai shari’a Wada ya kama shi da laifi inda ya yanke masa hukunci shekaru biyar akan tuhuma ta farko ta cin amana inda ya wanke shi a sauran tuhumar.

Alfijr

Har wa yau, kotu ta umarce shi da ya mayar da kudi har Naira miliyan ashirin da biyu, da dubu dari da  tara.