Kotu Ta Tsare Wani Matashi Kan Zargin Da Cin Zarafi Da Ɓata Sunan Gwamnan Kano

Wani matashi ya gurfana a gaban kotun shari’ar musulinci dake zaman ta a unguwar Kwana huɗu Kano, bisa tuhumar sa da cin zarafi da tayar da hatsaniya cikin al’umma da kuma ɓata suna wanda hakan ya saɓa da sashi na 312, 188 da 278 na kundin SPCL.

Alfijir Labarai ta rawaito tunda fari matashin mai suna Tasi’u Sule Gano, ya gurfana ne kan zargin sa da hawa shafin sada zumunta na Facebook, in da ya ci zarafin gwamnan jahar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf da kuma Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso ta hanyar yi musu zagin tsamar nama.

Hon. Umar Musa Gama, ne ya shigar da ƙorafin a ofishin yan sanda sashin binciken manyan laifuka dake Bompai.

Mai gabatar da ƙara Aliyu Abidin Murtala ya karanto masa ƙunshin tuhumar da ake yi masa inda ya musanta zargin.

A nasa bangaren Mai shari’a Malam Nura Yusuf Ahmad ya yi umarnin tsare shi a gidan gyaran hali da tarbiya, kuma ya dage karar zuwa ranar 26 ga watan Yuli 2023 domin gabatar da shaidu.

Oddity 24

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

One Reply to “Kotu Ta Tsare Wani Matashi Kan Zargin Da Cin Zarafi Da Ɓata Sunan Gwamnan Kano”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *