Kotu Ta Yanke Wata Mata Hukuncin Share Makaranta Na Wata 6

Alfijr ta rawaito wata kotun Majistare da ke zamanta a garin Ota na Jihar Ogun, ta umarci wata mata da ta share harabar makarantar Iju-Ebiye na tsawon wata shida, saboda tura ’yan daba su daki shugaban makarantar.

Matar, mai suna Biola Joshua mai kimanin shekara 40 dai, ana zarginta ne da daukar hayar ’yan daba zuwa makarantar don cin zarafin malamin.

A kunshin tuhumar, ’yan sanda sun tuhume ta da laifin hada baki, cin zarafi da kuma tayar da zaune tsaye.

Alfijr

’Yar sanda mai shigar da kara, sifekta Cynthia Ejezie, ta shaida wa kotun cewa wacce ake zargin tare da dan nata da wasu da yanzu haka suka arta ana kare, sun aikata laifin ne da misalin karfe 2:00 na ranar 11 ga watan Maris din 2022 a makarantar ta Iju-Ebiye.

Cynthia ta kuma ce wacce ake zargin da sauran wadanda suke tare dai sun lakada wa shugaban makarantar da kuma malamin da ke kula da lafiyar dalibai dukan kawo wuka.

Alfijr

Hakan, a cewar ta, sun samu munanan raunuka a jikinsu, baya ga tayar da hankulan dalibai suna tsaka da karatu a cikin makarantar.

Mai Shari’a Shotunde Shotayo, da take yanke hukunci, ta umarci matar da ta share makarantar kullum tun daga karfe 8:00 na safe har zuwa 11:00 na safe, tsawon wata shida.

Alfijr

Sai dai ta ba da zabin biyan tarar N30,000 a maimakon sharar, wadanda za a ba malaman da aka ci zarafin nasu.

Kamar yadda jaridar Aminiya ta wallafa

Slide Up
x