Kotun Koli Ta Sanya Ranar Yanke Hukuncin Shari’ar Zaben Jihar Kaduna

IMG 20240111 234351

Kwanaki biyu bayan yanke hukuncin zaben jihar Kano, Kotun Koli ta sanya ranar raba gardama a shari’ar zaben Kaduna Kotun ta sanya ranar Alhamis 19 ga watan Janairu a matsayin ranar yanke hukuncin karshe kan takaddamar zaben Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Uba Sani ya yi nasara a Kotun Daukaka Kara a matsayin halastaccen zababben gwamna a jihar

Alfijir labarai ta rawaito Kotun ta sanar da ranar Alhamis 19 ga watan Janairu a matsayin ranar yanke hukuncin da ake yi a jihar kan zaben gwamna. Kotun Koli za ta yanke hukunci a shari’ar Kaduna ranar Alhamis.

Isah Ashiru Kudan wanda ya yi takara a jami’yyar PDP shi ke kalubalantar zaben Gwamna Uba Sani na jam’iyyar APC a jihar.

A kwanakin baya, Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Uba Sani a matsayin halastaccen zababben gwamna a jihar. Har ila yau, ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam’iyyar PDP, Ashiru Kudan saboda rashin gamsassun hujjoji a shari’ar.

Wannan na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan yanke hukuncin zaben gwamnan Kano da ta dauke hankulan mutane a Najeriya baki daya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *