Kotun Musulunci Ta Hana Auren Wata Budurwar A Kano


Alfijr ta rawaito hakan ya biyo bayan karar da Wani matashi  ya kai kotun, yana rokon Kotun Musulincin da ke zamanta a unguwar Hotoro a Kano, ta hana budurwarsa auren wani ba shi ba, saboda kudin da ya kashe mata.

Sa yake bayani ya ce ya kashewa masoyiyar tasa makudan kudade saboda tsananin kaunar da yake mata, ashe ita yaudar sa take yi ba son Allah take masa ba!

Kwanci tashi sai ya labari a gari ya isheshi cewa masoyiyar tasa za tayi auri wani ba shi ba.

A nasa bangaren Mai Shari’a Salisu Isa Kura ya amince da bukatar matashin, in da yace a tsaya cak, har sai Kotu ta kammala bincike da take a kan lamarin.

Freedom Radio

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Best seller Channel
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *