Kudawan Dambe Za Su Yi Taro Don Zakulo Fitattun Jarumai

Alfijr ta rawaito Kungiyar magoya bayan damben gargajiya ta kasa bangaren Kudu za ta gabatar da taro ranar Asabar Kano.

Kungiyar karkashin jagoranci shugabanta Alhaji Adamu Mohammed Tanko za ta yi taron a Kabo guest in.

Shugaban ya ce za su gudanar da taron domin kamo bakin zare kan matsalar da take ci musu tuwo a kwarya.

Haka kuma kungiyar za ta gana da juna a matakin sada zumunta a tsakanin mambobinta.

Alhaji Tanko Daraktan magina Maga yakin Barden Zazzau Suleja ya ce matsalar da take gabansu ita ce ta karancin ‘yan wasa.

Ya kara da cewar manyan ‘yan wasan Kudawa na tsufa wasu sun yi ritaya, amma suna rasa matasa da suke maye gurbinsu.

Ya kara da cewar damben gargajiya wasa ne na Hausa mai dadande tarihi, ba za su nade hannu a mance da al’adar ba.

Ana buga dambe ne tsakani ‘Yan wasa daga Kudu da Arewa da kuma bangaren Guramada.

Babu dama dan wasan Kudu ya kara da dan uwansa daga Kudu ko Arewa da Arewa ko Guramada da Guramada, sai dai wani lokaci sukan dambata a tsakaninsu idan rana ta baci.

Tun bayan da manyan ‘yan wasa daga bangaren Kudu suka yi ritaya irinsu Shagon Bahagon Kanawa da Shagon Mada da Abdurrazak Ebola, daga lokacin ta rasa ‘yan wasan dake tare mata yakin dambe.

Alhaji Tanko ya ce za su tallafi ‘yan wasa don ganin sun ci morar damben gargajiya da suka dauka sa’a don magance zaman banza.
Ana buga wasan a fadin Najeria, inda mai gidan dambe kan basu kudin abinci da na dakin kwana iya girmanka da sunanka da jarumturka iya kudinka.

Wani lokaci magoya bayan ‘yan wasa ne ke daukar nauyinsu domin kara musu kwarin gwiwa.

Wasan damben Gargajiya mai dan karen farinjini ya daukaka a fadin Najeriya har ma an saka shi cikin wasannin kasa da ake kura National Sports Festival.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *