Kwankwaso Ya Zargi Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu Da Shirin Ruguza Jihar Kano,

FB IMG 1718698222689

Akwai mutanen Kano, makiya jihar, wadanda ke fama da tabin hankali,

Alfijir labarai ta ruwaito sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya zargi Gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC da bin muguwar shawara daga makiyan jihar Kano.

Jawabin na Kwankwaso ya zo ne a matsayin martani ga rikicin masarautar da ke ci gaba da ruruwa, Inda jami’an tsaron Gwamnatin tarayya da ke da alhakin tabbatar da .zaman lafiya ke marawa tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero baya.

Da yake jawabi a wajen bikin ƙaddamar da gina titunan karkara mai tsawon kilomita 82 a mahaifarsa Madobi, Kwankwaso ya bayyana cewa al’ummar Kano za su bijirewa duk wani yunkuri na kawo cikas ga Gwamnatin jihar.

“Muna da yawan mabiya saboda mutane sun yi imani da mu. Mu masu goyon bayan jama’a ne, kuma Gwamnatin NNPP ta kuduri aniyar yi musu hidima a duk inda suka zabe mu,” inji Kwankwaso.

Ya ci gaba da cewa, “Ba za mu nade hannayenmu muna kallon makiyan jihar suna lalata zaman lafiya a jiharmu mai daraja ba. Za mu yi duk mai yiwuwa don tallafa wa gwamna don samun nasara. Ina farin ciki da cewa bai shagala ba kuma yana mai da hankali kan cimma burinsa.

“Akwai mutanen Kano, makiya jihar, wadanda ke fama da tabin hankali, kuma suna ba gwamnatin tarayya shawarar karbe Kano ta hanyar gaggawa. Wannan hauka ne na babba, wanda nagari, masu son zaman lafiya, masu kishin Kano za su bijirewa.

“Yayin da muke tunkarar shekarar 2027, wasu ‘yan siyasa masu tsananin son zuciya sun riga sun shiga wani shiri na kawo cikas. Mun gwammace mu duka mu yi asara da kyale su su murkushe mu Muna jajircewa duk wanda yake ganin za su iya cin zarafin mu a siyasance ya tabbatar da cewa a shirye muke mu yi fada.

“Ba ma tsoron fita daga mulki domin za mu ci gaba da zama ‘yan siyasa a cikin gwamnati Ba za mu iya guje wa kaddara ba. Mu mutane ne, mun san abin da ya dace a gare mu, kuma za mu bi shi da karfi,” tsohon Gwamnan Jihar Kanon ya sha alwashin.

Jagoran na NNPP na kasa ya ci gaba da cewa Gwamnatin Tarayya tana sauraron ’yan siyasa marasa kishin kasa daga Kano, wadanda za su taimaka wajen gazawarta. Ya kuma jaddada cewa al’ummar Kano za su bijirewa duk wani yunkuri na kawo cikas ga ayyukan da kundin tsarin mulki ya rataya a wuyan Gwamna.

“Muna shirye don tattaunawa, Domin sasantawa, amma ba za mu yarda da tsoratarwa ko cin zarafin siyasa ba. Mun san yadda ake yin siyasa, kuma muna da dukkan abin da ya dace don kare kanmu daga duk wani sharri,” in ji Kwankwaso.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *