Labari Mai Dadi! Kotun Ƙolin Najeriya Ta Tabbatar Da Bawa Ƙananan Hukumomi Kudadensu

Screenshot 20240711 113121 Chrome

Kotun Ƙolin Najeriya ta ce riƙe kuɗin ƙananan hukumomi da gwamnaonin jihohin ƙasar ke yi ya saɓa wa kundin tsarin mulki.

Alfijir labarai ta ruwaito hukuncin da kotun ta yanke  ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Emmanuel Agim, ya ce kotun ta fahimci cewa gwamnatocin jihohin ƙasar sun shafe fiye da shekara 20 ba tare da sakar wa ƙananan hukumomin mara ta fuskar kuɗaɗensu ba.

Alƙalin kotun ya ci gaba da cewa tun tsawon wanan lokaci, ƙananan hukumomin ba sa samun kuɗaɗen da ya kamata su samu daga gwamnonin jihohin ba, waɗanda ke kashe kuɗin ta hanyar yin ayyuka a madadin ƙananan hukukomin.

Mai shari’a Agim ya ce dole ne ƙananan hukumomin ƙasar 774 su riƙa amfani da kuɗaɗensu da kansu ba tare da sa katsalandan daga gwamnonin jihohi ba.

Haka kuma alƙalin ya yi watsin da ƙorafin da gwamnonin suka yi ta bakin lauyoyinsu.

Gwamnatin tarayyar ta kuma buƙaci kotun ta dakatar da gwamnonin jihohin ƙasar, daga rushe zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *