Labarin Rayuwa: Ƴan Majalisar Wakilai Sun Rage Kashi 50 A Albashinsu

Screenshot 20240718 172457 Facebook

Mambobin Majalisar Wakilai sun amince su rage kashi 50 cikin 100 na albashinsu na tsawon watanni shida a matsayin hadin kai da sadaukarwar da suke yi na tallafa wa matsalolin tattalin arziki da yunwa da ‘yan Najeriya ke fama da su a halin yanzu.

Alfijir labarai ta ruwaito hakan ya biyo bayan amincewa da wani gyaran kudiri da mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Okezie Kalu ya gabatar kan bukatar ‘yan majalisar su sadaukar da kashi 50% na albashin su na Naira dubu 600 duk wata don tallafa wa ‘yan Najeriya duba da halin kuncin da ake ciki a majalisar. ƙasa.

Rokon na Kalu da aka yi wa gyaran fuska ta kasance ne ga kudirin da dan majalisa Isiaka Ayokunle ya gabatar na yin kira ga masu goyon bayan zanga-zangar da aka shirya yi a fadin kasar da su yi watsi da ra’ayin tare da shiga cikin tattaunawa da gwamnati.

Mataimakin shugaban majalisar ya ce za a yi amfani da rage albashin ne domin tallafa wa kokarin gwamnatin tarayya na magance tsadar kayan abinci a kasar da nufin magance wahalhalun da ‘yan Najeriya ke ciki.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, ta hanyar rage musu albashi da kashi 50 cikin 100, ‘yan majalisar su 360 za su rika sadaukar da Naira miliyan 108 duk wata na tsawon watanni shida masu zuwa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *