Jami’an hukumar yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi ta NDLEA a Kano sun shiga hannu bayan sun harbe wata budurwa mai shekaru 19, Patience Samuel, a unguwar Jaba a kano
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:55 na dare a ranar Laraba, inda rahotanni suka nuna cewa jami’an ‘yan sanda sun kai ɗauki, suka kwashe ta zuwa Asibitin koyarwa na Abdullahi Wase, inda aka tabbatar da rasuwarta.
An kama jami’an biyu, Nass Ridwan Usman mai shekaru 23 da Ismaila Yakubu mai shekaru 26, waɗanda ke aiki a shalƙwatar NDLEA a Kano.
Har yanzu NDLEA ko ‘yansanda ba su fitar da wata sanarwa dangane da lamarin ba.
LeadershipHausa
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ