Majalisar dokokin jihar Kano a ranar Asabar ta karyata jita-jitar da ke yawo na cewa ana shirin tsige mataimakin Gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam-Gwarzo.
Majalisar ta bayyana rahotannin a matsayin “marasa tushe kuma masu haifar da ruɗani,” tana mai jaddada cewa babu wani shiri ko yunƙuri makamancin haka da ke gudana.
Da yake zantawa da ’yan jarida a Kano, mai magana da yawun Kakakin Majalisar, Kamaluddeen Shawai, ya ce labaran da ke yawo an ƙirƙire su ne domin haifar da tashin hankali a jihar.
“Babu wani kudiri ko yunƙuri a cikin Majalisar na tsige Mataimakin Gwamna kwata-kwata.
“Waɗannan rahotanni ƙarya ne, kuma ya kamata al’umma su yi watsi da su. Mataimakin Gwamna na ci gaba da aikinsa tare da cikakken goyon bayan Majalisar,” in ji shi.
Ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da kuma jama’a da su rika tantance bayanai kafin yaɗa su, yana mai jaddada cewa sahihin rahoto yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiyar siyasa a jihar.
Malam Shawai ya ƙara da cewa Majalisar na mai da hankali ne kan ayyukan dokoki da kuma sa ido, ba wai dabarun siyasa na zato-zato ba.
“Abin da ya fi ba mu muhimmanci shi ne kyakkyawan shugabanci da yi wa al’ummar Kano hidima, ba yaɗa jita-jita ba,” in ji shi.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t