Majalisar Malamai ta yanke hukuncin kan danbarwar masallaci da Bin Othman a kano

IMG 20250219 111646

Shugaban majalisar malamai ta Kasa Sheik Ibrahim Khalil ya bayyana cewa bayan zama da dukkanin bangarorin da danbarwar Sabon masallacin Sahaba dake kundila a Kano, majalisar ta yanke hukuncin na karshe a kan rikicin.

” Mun yanke hukuncin Sheikh Muhammad Bn Othman zai koma masallacinsa na Sahaba , shi kuma mai kifi da sauran mutanensa za su cigaba da rike na su masallacin na jami’urrahman”.

Malam Ibrahim Khalil ya bayyana hakan ne lokacin da yake bayyana sakamakon zaman da suka yi ga manema labarai a Kano.

Ya ce Sheikh Muhammad Bin Othman ya Amince zai cigaba da jagorantar sallah a tsohon masallacinsa na Sahaba dake kundila, yayin da su kuma su mai kifi za su cigaba da gudanar da harkokin masallacinsun na jami’urrahman.

Ya kuma godewa dukkanin jami’an tsaro musamman DSS saboda rawar da suka taka wajen tabbatuwar wannan sulhun.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *