Majalisar Wakilai Ta Nemi A Gudanar Da Babban Zabe A Watan Nuwanba 2026.

IMG 20251014 WA0003

Daga Aminu Bala Madobi

Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta Najeriya ta ba da shawarar a gudanar da zaɓen 2027 a watan Nuwamba 2026, wato watanni shida kafin wa’adin gwamnatin yanzu ya ƙare. Wannan na cikin daftarin gyaran dokar zaɓe ta 2025 da aka gabatar a taron jin ra’ayoyi a Abuja.

Manufar gyaran ita ce tabbatar da cewa duk ƙarar zaɓe sun ƙare kafin ranar rantsarwa ta 29 ga Mayu, 2027. Sabon tanadi zai rage lokacin sauraren ƙarar zaɓe daga kwanaki 180 zuwa 90 a kotunan zaɓe, da daga 90 zuwa 60 a kotunan daukaka ƙara.

Haka kuma, gyaran dokar na son samar da zaɓe na farko (early voting) ga jami’an tsaro, ma’aikatan INEC, ‘yan jarida da masu sa ido, mako biyu kafin ranar zaɓe.

An kuma tanadi hukunci ga jami’an da suka karya doka, ciki har da tara ₦1 miliyan ko shekara ɗaya a kurkuku ga wanda ya bayar da takardun sakamako ko ƙuri’u ba tare da hatimi ba.

Gyaran dokar zai kuma tilasta amfani da tsarin aika sakamakon zaɓe ta lantarki da hannu (e-transmission), domin tabbatar da gaskiya da rage rikicin bayan zaɓe.

Hukumar INEC da wasu ƙungiyoyi sun goyi bayan shirin, suna cewa zai ƙara sahihanci ga tsarin dimokuraɗiyya.

A baya bayan nan, an ta samu muhawara kan wani shirin da ke son dukkan zaɓe a Najeriya su gudana rana ɗaya a 2027 — shirin da jam’iyyun adawa suka goyi bayan sa, amma jam’iyyar APC mai mulki ta soki shi tana ganin zai iya haifar da matsaloli.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *