An ja hankalina kan wata wasika da ake ikirarin an rubuta min, amma abin mamakin sai takardar take yawo a kafafen sada zumunta kafin ta iso gare ni ta hanyar da ta kamata.
Ina ganin hakan bai dace ba, ace Ministan Tarayyar Najeriya ko kuma ma duk wani mamba na jam’iyya ya fara gani tare da karanta wasikar da aka rubuta masa a kafafen sada zumunta kafin ta iso gare shi a hukumance.
Bugu da ƙari, wasikar ba ta ambaci wata takamaimiyar magana, aiki, ko halin da ake zargi na da aikata wa ba.
Shima kuma gargadin da aka ambata kan abinda ake zargi na dashi gaba ɗaya babu bukatar mayar da martani ta hanya mai ma’ana ko akasin haka ba.
Don haka, a matsayi na na ɗan Najeriya, ina da cikakkiyar dama da iko wadda kundin tsarin mulki ya bani na bayyana ra’ayoyi na na kashin kai na.
Ban taɓa wani ikirari kai tsaye ko a kaikaice na cewa sai an bi wane, ko dole abi ra’ayin wane a madadin jam’iyya ba, sam sam. Duk maganar da zan yi, ina yin ta ne a matsayi na na mutum mai cikakken iko.
Haka kuma, ina da iko da damar ci gaba da yada manufofi masu amfani da kuma tsarin Renewed Hope na shugaban kasa.
Na kasance mai kare martaba da muhibba ta shugaban kasa kuma babban Kwamandan Rundunonin Najeriya, mai girma Bola Ahmad Tinubu, GCFR, kuma zan ci gaba da yin hakan cike da aminci da biyayya.
Har yanzu ina nan a matsayin mamba nagari mai biyayya ga jam’iyyarmu ta APC, kuma ina ƙoƙari wajen yadawa tare da aiwatar da ayyukan cigaban al’umma da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ke aiwatarwa, domin amfanin jam’iyyar tamu da kuma al’ummar Najeriya baki ɗaya.
Ina fatan za a karbi wadannan bayanai nawa cikin mutuntaka da kuma girmamawa.
Rt. Hon. Yusuf Abdullahi Ata, karamin Ministan ma’aikatar gidaje da bunkasa birane na Najeriya.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t