Matar Na Tuba! Mataimakin Gwamnan Kano Ya Nemi Afuwar Nuhu Ribado

FB IMG 1716796970945

Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamaret Aminu Abdussalam Gwarzo ta ba wa Mashawarcin Shugaban Kasa kan sha’anin Tsaro Nuhu Ribadu hakuri kan zargin sa hannunsa a rikicin masarautun jihar.

Alfijir labarai ta ruwaito mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdulsalam a ranar Asabar yana zargi Ribadu da yunkurin dawo da Sarkin Kano Aminu Ado Bayero kan kujerarsa bayan gwamnatin jihar ta sauke shi tare da sauran sarakunan jihar.

Daga bisani Ribadu ya nesanta kansa da kuma ofishinsa daga rikicin, sannan ya yi barazanar maka mataimakin gwamnan a kotu.

Mataimakin gwamnan ya baiwa Ribadon hakuri ne yayin wani taron manema labarai a daren Lahadi.

Bayan haka ne mataimakin gwamnan ya ba da hakuri ga Ribadu yana mai cewa yaudarar gwamnatin aka yi da bayanan da aka bata ba sahihai ba.

” Don haka yanzu a madadin ni kai na da gwamnatin jihar kano Muna baiwa mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro hakuri, kuma muna bashi tabbacin za mu cigaba da ba shi hadin kai da goyon baya don ya gudanar da aikin sa yadda ya kamata”.

“Mun kara zurfafa bincike inda muka gano cewa yaudarar mu aka yi, saboda haka, a madadin gwamnatin Kano, mana ba da hakuri ga Mashawarcin Shugaban Kasa kan Sha’anin Tsaro,” in ji mataimakin gwamnan.

Gwamnatin jihar ta kuma bukaci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya baki kada abin ya kara rincabewa fiye da haka.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/F9mRRuOf58G3MlLKsNCJbL

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *