Wasu fusatattun matasa a garin Lafiagi, hedikwatar karamar hukumar Edu da ke Jihar Kwara, sun kai farmaki ranar Litinin zuwa Fadar Sarkinsu, wato Sarkin Lafiagi, da kuma Ofishin Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), inda suka cinna musu wuta sakamakon yawaitar sace-sacen mutane da ke faruwa a yankin ba tare da dakilewa ba.
Tashin hankali ya mamaye al’ummar Lafiagi a ranar Litinin, lamarin da ya haifar da zanga-zangar matasa domin bayyana fushinsu kan sace wani sanannen ɗan kasuwa a yankin.
Fusatattun matasan sun fara zanga-zangar ne da safiyar jiya Litinin kan sabon lamarin sace mutum, inda suka toshe hanyoyi, suka kunna tayoyi da suka ƙone, tare da neman gaggawar ɗaukar matakin gwamnatin jihar kafin daga bisani su bankawa Fadar Sarkin da ofishin NDLEA wuta.
A wani faifan bidiyo da ya yadu, masu zanga-zangar sun ambaci sace wani matashi da ke aikin kasuwancin POS a matsayin karin hujja da ke nuna tabarbarewar tsaro a yankin.
Wasu mazauna Lafiagi sun shaida wa Vanguard cewa an sace Alhaji Chemical ne daga gidansa da ke unguwar Taiwo da misalin karfe 1:00 na dare, inda wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka mamaye yankin.
Da aka tuntube shi, Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kwara, Mista Adekimi Ojo, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa yana cikin garin Lafiagi ranar Litinin tare da Kwamandan Rundunar Sojoji ta 22 da ke Sobi, Ilorin. Ya bayyana cewa wasu bata-gari ne suka shirya zanga-zangar inda suka lalata wasu gilashin Fadar Sarkin sannan suka ƙone ofishin NDLEA.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD