Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin, ya bayyana fatansa na amincewar shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kudurin dokar hukumar raya yankin arewa maso yamma (NWDC) domin magance dimbin kalubalen da yankin ke fuskanta.
Alfijir labarai ta ruwaito Sanata Barau, wanda ya dauki nauyin kudirin, ya bayyana cewa za a mika kudirin zuwa fadar shugaban kasa domin amincewa, bayan da majalisun biyu suka amince da shi.
A wata sanarwa da ya fitar a Jiya Talata ta bakin mai ba shi shawara na musamman kan Harkokin yada labarai Ismail Mudashir, Barau ya bayyana cewa amincewa da kudirin ya yi daidai da kudurin shugaba Tinubu na kawo sauyi ga kasar nan da kuma jagorantar ta zuwa ga ci gaba da wadata.
Kwanakin baya ne majalisun biyu suka amince da kudurin dokar a wani bangare na ƙoƙarin magance kalubalen da jihohin Arewa maso Yamma ke fuskanta: Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Jigawa, Sokoto, da Zamfara.
Da yake bayyana yankin Arewa maso Yamma a matsayin kwandon abincin kasar, Sanata Barau ya jaddada cewa hukumar za ta yi kokarin dawo da kayayyakin more rayuwa da rikicin Boko Haram da ‘yan bindiga suka lalata a yankin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj