Muna Goyon Bayan A Raba Nijeriya – In Ji Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa

IMG 20240204 064944

Shugaban ƙungiyar gamayyar kungiyoyin matasan arewa Ashiru shariff Nastura yayin da yake tattaunawa da manema labarai ya jaddada goyon bayan su da a zauna a raba Nijeriya kowa ya kama gabansa.

Alfijir labarai ta rawaito Ashir shariff Nastura ya kawo misalin cewa a lokacin da akayi End Sars aka kona tirela kusan sittin da wani abu, da yan arewa sunyi irin wannan yunkurin sun janye kai kayan abincin an tsaya anyi maganganu da yanzu an biya su diyar abubuwan da akayi musu na ɓarna na rayuka da dukiyar su amma akayi burusi.

Shariff yace yanzu abinda muka so kowa ya gane a Nijeriya, mufa ba dole sai anyi zaman kasar nan daya ba, mu bai dame mu ba, shiyasa tun ainihii kakanmu da ya gina Arewancin Nijeriya sir. Ahmadu Bello Sardauna yace wannan zalunci ne, kuskure ne hada kudancin Nijeriya da Arewan Nijeriya a matsayin kasa Daya, muka ki goyan bayansa.

Mu a zo a raba kasar nan lami lafiya kowa ya kama gabansa, ba sai anyi amfani da yaƙe-yaƙe da tashin hankali kafin a raba kasa ba. In Ji Nastura.

Mu muna goyon bayan azo a zauna a duba kadarorin kasar nan a raba ko wane yanki a bashi nashi hakinsa, a bashi a raba kasa cikin kwanciyar hankali , ba tare da sai anyi tashin hankali ba.

Ashir ya kara da cewa, kuma mun sha fadar wannan maganar ba zamu yarda da zubar da jini a Najeriya ba, an dauki ran mutumin arewa da, dukiyarsa da jininsa da rayuwar sa ba’a bakin komai ba.

Ba wanda zai dora mana wannan tsarin mu yadda, ba’a isa ba kowa ye shi, gara a raba kasar kowa ya kama gabansa yaje yaga abinda zaiwa kansa, ba zamu Kara yadda a kashe mutumin arewa ba, a kone dukiyarsa aci mutucinsa, bamu goyi baya ba.- inji Ashir shariff Nastura

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *