Salma Muhammad Jega
Idan ba a samu wani sauyi na ƙarshe ba, gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, zai fice daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC a makon farko na watan Janairun 2026.
Ficewar Mista Yusuf za ta kawo ƙarshen alaƙarsa ta kusan shekaru arba’in da mai gidansa a siyasa Rabiu Kwankwaso.
Kasancewar shi kaɗai ne gwamna a jam’iyyar NNPP, ficewarsa za ta sa a zahiri jam’iyyar ta ɓace daga jerin jam’iyyun da ke riƙe da gwamnatocin jihohi a Nijeriya.
Da yake jam’iyyar APC ta shirya gudanar da tarukan zaɓen shugabanninta a watan Fabrairu, gwamnan ya kammala shirinsa na shiga tarukan domin karɓe cikakken iko da jam’iyyar a jihar.
Domin ƙara wa ɓangarensa ƙarfin siyasa, majiyoyi sun shaida wa wannan jarida cewa gwamnan ya dade yana shirya dabaru a ɓoye domin samun goyon bayan ‘yan Majalisar tarayya, majalisar dokokin Jihar da shugabannin ƙananan hukumomi.
“Ɗan Majalisar Wakilai guda ɗaya da na tabbatar zai ci gaba da kasancewa tare da Kwankwaso shi ne surukinsa, wakilin mazabar Tarauni. Wakilan Nassarawa, Ungogo da Kumbotso kuwa suna shakku, suna auna yanayin siyasar,” in ji wata majiya da ta san abin da ke faruwa.
DAILY NIGERIAN ta gano cewa aƙalla ‘yan Majalisar dokokin Jihar NNPP 25 (biyu daga cikinsu sun rasu) daga cikin 27, ciki har da Kakakin Majalisar, Yusuf Falgore, sun amince da shirin gwamnan na ficewa daga jam’iyyar.
Sai dai majiyoyin sun ƙara da cewa gwamnan ya samu goyon bayan adadi mai yawa na shugabannin ƙananan hukumomi. “Wasu daga cikin shugabannin ƙananan hukumomin a halin yanzu suna biyayya ga Kwankwaso, amma zan iya tabbatar maka cewa a ƙarshe kusan dukkansu za su bi gwamnan,” in ji majiyar.
Yayin da shirin ficewar gwamnan ke ƙara ƙarfi, Mista Kwankwaso ya kira ‘yan Majalisar Dokokin Jihar zuwa wani taro a gidansa da ke Miller Road a ranar Juma’a.
DAILY NIGERIAN ta gano cewa a yayin taron, Mista Kwankwaso ya shaida musu cewa a bayyane yake gwamnan na shirin barin NNPP ya koma APC, don haka duk wanda ya zaɓi bin gwamnan ya yi hakan.
Mista Kwankwaso ya nuna takaicinsa, yana cewa ba a ba shi hujja mai gamsarwa kan dalilin da ya sa za su koma APC ba, yana mai jaddada cewa sun ci zaɓe ne da babu wani sai Allah. “Shin Allah da ya ba mu mulki a 2023 ba zai kasance tare da mu a 2027 ba?” in ji Kwankwaso, kamar yadda aka rawaito yana tambaya.
DAILY NIGERIAN ta gano cewa a ƙarshen taron, ‘yan majalisar sun amince su gana da gwamnan domin a ba da dama ta ƙarshe ga tattaunawa, ta yadda duk wani shawarar siyasa da gwamnan zai ɗauka, a ɗauke ta tare da Kwankwaso.
Sai dai wata majiya ta shaida wa wannan jarida cewa lokacin da ‘yan majalisar suka nemi ganawa da gwamnan bayan taron na Miller Road, gwamnan ya ce ya riga ya ji duk abin da ya faru a taron, kuma shawarar da ya yanke na shiga APC ba za a iya sauya ta ba.
Yiwuwar tsige mataimakin gwamna
Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam, na iya zama mutum na farko da zai faɗa cikin guguwar siyasar da ke shirin afkawa jam’iyyar NNPP a Kano.
Majiyoyi sun ce a matsayin wani ɓangare na shirin gwamnan na samun goyon bayan manyan jiga-jigan APC a Kano, ana shirin miƙa sunan tsohon ɗan takarar mataimakin gwamna na APC a zaɓen 2023, Murtala Sule-Garo, domin maye gurbin Abdulsalam. Haka kuma, ana shirin miƙa sunan tsohon ɗan takarar gwamna na APC a 2023, Nasiru Gawuna, a matsayin ɗan takarar Sanata na Kano ta tsakiya a 2027.
Tun bayan hukuncin Kotun Koli kan zaɓen gwamnan Kano, gwamnan ya yi ƙoƙari sosai wajen shawo kan Kwankwaso da ya koma APC.
A watan Nuwamban bara, DAILY NIGERIAN ta rawaito rikicin da ke ƙara tsananta a NNPP ta Kano, inda gwamnan ya kaurace wa taruka tare da ƙin ɗaga kiran wayar ubangidansa, Rabiu Kwankwaso.
A shekarar 2024, taken siyasa na “Abba Tsaya da Kafarka” — wato Abba, tsaya da ƙafarka, ko kuma a ma’ana mafi ƙarfi, Abba, rabu da Kwankwaso — ya yi fice a Kano, yayin da kiraye-kiraye daga cikin jam’iyyar da wajen ta ke ƙara ƙarfi na neman gwamnan ya zama mai cin gashin kansa.
Gwamnan, duk da ya sha alwashin biyayya ga Kwankwaso, ya musanta rahotonmu na Nuwamba 2024 tare da nesanta kansa daga ƙungiyar Abba Tsaya da Kafarka.
Kakakin gwamnan, Sanusi Dawakintofa, bai kai ga amsa kiran waya da saƙon tes ɗin da wakilinmu ya aika masa ba, domin jin martaninsa kan lamarin.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t