Najeriya ta buƙaci kamfanin Binance ya biya ta diyyar dala biliyan 10

FB IMG 1709284801000

Gwamnatin Najeriya ta buƙaci shafin musayar kuɗin intanet na Binance ya biya ta kuɗi dalar Amurka biliyan 10 a matsayin tara, bisa iƙirarin da gwamnatin ta yi na asarar da ta tafka sanadiyyar ayyukan shafin.

Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnatin ta zargi shafin na Binance da zuzuta farashin musayar kuɗaden waje ta hanyar yin hasashe maras tushe da kuma shaci-faɗin darajar naira, lamarin da ya sa darajar naira ta zube da kimanin kashi 70 cikin 100.

A ranar Alhamis ne gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa tana tsare da wasu manyan jami’an shafin Binance biyu, waɗanda jami’an tsaro ke yi wa tambayoyi bisa zargin shafin da zama wata kafa ta halasta kuɗaɗen haram da kuma samar da kuɗi ga ƴan ta’adda.

Wannan ya biyo bayan iƙirarin da Babban Bankin Najeriya ya yi a ranar Talata cewa kuɗi kimanin dala biliyan 26 ne aka yi safarar su ta shafin Binance daga Najeriya zuwa wasu wuraren da ba a sani ba.

Bayo Onanuga, wanda shi ne mai magana da yawun shugaban Najeriya ya shaida wa BBC cewa: “Jami’an na Binance na bai wa gwamnati haɗin kai ta hanyar samar da bayanai”.

Har yanzu dai Binance bai ce komai ba game da batun tsare jami’an nasa biyu a Najeriya.

Babban Bankin Najeriya na shan matsi wajen ganin ya daidaita darajar naira wadda farashinta ke ci gaba da tangal-tangal.

Faɗuwar darajar naira ta ƙara damalmala halin tsadar rayuwa da al’ummar Najeriya ke ciki sanadiyyar tashin farashin kayan masarufi da na abinci da sufuri, wanda ya haifar da jerin zanga-zanga a wasu yankunan ƙasar.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *