NDLEA Ta Gano Kamfanin Hada A-Kuskura Tare Da Wasu Miyagun Kwayoyi


Alfijr ta rawaito hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyin a Nijeriya NDLEA ta ce ta gano wani kamfani da ake hada A-kuskura a garin Mubi na Jihar Adamawa.

Hukumar ta ce kamfanin ya gawurta domin har yana fitar da A-kuskura zuwa kasashen Chadi da Kamaru da Jamhuriyyar Nijar.

Kakakin hukumar ta NDLEA Femi Babafemi ne ya sanar da kamun a wata sanarwa da ya fitar mai kunshe da bayanai kan kamen da suka yi na miyagun kwayoyi.

Ya kara da cewa a lokacin da jami’an nasu suka kai samamen, ana cikin aikin hada A-kuskura.

Haka kuma hukumar ta ce ta kai samame a wani kango da ke cikin wani daji a birnin Ala da ke Akure a Jihar Ondo inda ta gano akalla buhu bakwai na tabar wiwi.

Baya ga haka kuma akwai dauri 126 na tabar wiwi nau’in ‘Canadian Laud’ cikin mota kirar Corolla da aka yi safararta daga Jihar Toronto ta Canada. An kama wiwin ne a tashar ruwa ta Tincan da ke Legas.

Hakazalika a Jihar Benue hukumar  ta kama kwalaben maganin tari na codeine 859 wadanda nauyinsu ya kai kilo 117.3 wadanda ake zargin wani dillalin kwayoyi ne ya jefar da su kimanin kilomita biyu kafin shingen binciken NDLEA da ke hanyar Enugu zuwa Otukpo.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *