NDLEA Ta Kama Abubuwa Masu Fashewa 399, Da Haramtattun Kwayoyi A Neja

A kalla bama-bamai 399 ne jami’an hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa suka kwato daga hannun wani mai suna Asana Leke mai shekaru 39 a hanyar Mokwa-Jebba a ranar Alhamis, 7 ga watan Satumba.

Alfijir Labarai ta rawaito Wanda ake zargin, ya ce an mika masa bamabaman ne a wani wurin shakatawa da ke Ibadan a Jihar Oyo, domin a kai wa wani a Kaduna, tare da baje kolin, an mika shi ga hukumomin soji a Jihar Neja

Baya ga kokarin da ake yi na dakile yaduwar miyagun kwayoyi, hukumar ta NDLEA ta kuma ci gaba da yakin da take yi a makarantu, wuraren ibada, fadoji da sauran al’ummomin yankin da dai sauransu.

Mai Magana Da Yawun Hukumar NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a wani sakon email da ya aika wa wakilinmu.

Ya kuma yi nuni da cewa, jami’an NDLEA sun kama wasu kayan laifi da aka boye a cikin tumatur, da kuma methamphetamine da aka boye a cikin tufafin da aka yi yunkurin fitar da su zuwa Kasar Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa. 

Yayin da kwayar da aka boye cikin tumatur mai nauyin kilogiram 20 aka kama ta a ranar Juma’a, 8 ga watan Satumba, a shagon fitar da kayayyaki na SAHCO na filin jirgin saman Murtala Muhammed, Ikeja, a yayin jigilar an samu meth mai nauyin kilogiram 1.60 da aka kama a wani kamfanin jigilar kaya na Legas.

“Wani kaya mai nauyin gram 556 na Canadian Loud da aka aiko daga Kanada zuwa wani mutum mai suna Tunji Adebayo a Ikorodu, Legas, jami’an NDLEA na ofishin Darakta ayyuka da bincike na kasa da kasa, wadanda ke da alaka da kamfanonin jigilar kaya sun kama su.

A halin da ake ciki kuma, jami’an NDLEA sun kai samame unguwar wani kasurgumin dillalin kwaya da ke Akala, Mushin, Legas, Abdul Rauf, wanda ake kira ‘Na God’, inda aka kwato kilogiram 1,101 na Loud Ghana, tare da kama wasu mutum uku da ake nema ruwa a jallo.

A Jihar Ogun, wani bincike da aka gudanar ya kai ga cafke Yinka Azeez a Sabo Lafenwa, Abeokuta biyo bayan kama wata nau’in tabar wiwi mai nauyin kilogiram 41 daga hannun Titilayo Adetayo a mahadar Sagumu.

Har ila yau, akalla an kama wasu mutum biyu: Muhammad Aliyu mai shekaru 38 da Abdullahi Zakariyya mai shekaru 40 a hanyar Zaria zuwa Kano da Haye Arewa, Hotoro, Kano, da sama da kilogiram 426.5 na skunk.

Yayin da aka kama Onyeka Uzor, mai shekaru 25 a Idemili, Jihar Anambra, tare da skunk mai nauyin kilo giram 64.8 da Tramadol, wani wanda ake zargi, Destiny Irabor, an kama dauke da fiye da kilogiram 180 na opioids a cikin motarsa kirar Toyota Sienna.

A Kaduna, wasu mutum biyu; Ahmed Yusuf da Rilwan Nura, an kama su ne bisa laifin safarar tabar wiwi kulli 100 kilogiram 55 a hanyar Abuja.

A Jihar Edo, jami’an hukumar NDLEA sun kai farmaki dajin Ekudo dake Karamar Hukumar Onwude inda suka lalata gonakin tabar wiwi mai fadin hekta 4.236347.

Yayin da aka kama Onyeka Uzor, mai shekaru 25 a Idemili, Jihar Anambra, tare da kilo giram 64.8 na skunk da Tramadol, wani wanda ake zargi, Destiny Irabor, an kama shi dauke da fiye da kilogiram 180 na opioids a cikin motarsa kirar Toyota Sienna.

Hakazalika, jami’an ‘yansanda sun kai samame gidan wani Amuodu Egwehide, mai shekaru 40, da ke Iloje Okpuje, Karamar Hukumar Owan ta Yamma, inda suka kwato buhu 22 na skunk mai nauyin kilogiram 261.4, yayin da wata tsohuwa mai shekaru 60 Misis Eunice Egwehide, aka kama ta a garin a wannan rana tare da kilo giram 17 na tabar wiwi.

An kama wani da ake zargi mai suna Gapchiya Modu mai shekaru 26 da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 60 a kan hanyar Kano zuwa Nguru, Jihar Yobe, yayin da a Jihar Imo kuma an kwato buhuna 200 na irin wannan wiwi mai nauyin kilogiram 57 daga Usim Orji mai shekaru 45 a hanyar Aba-Owerri.

Bayan sama da watanni biyu ana sa ido, jami’an NDLEA sun kama wani basarake da ake nema ruwa a jallo, Idoko Ifesinachi, mai shekaru 40, da laifin shigo da Loud mai nauyin kila giram 76.9 na Canada Loud da aka kama a cikin wani akwati mai lamba MSDU6686346 a tashar Port Harcourt, Onne. Jihar Ribers. An kama shi a maboyarsa da ke Legas aka kai shi Fatakwal.

Leadership Hausa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *