NDLEA Ta Kama Jirgin Ruwa Makare Da Tabar Wiwi A Lagos

Hukumar NDLEA ta tabbatar da kama tabar wiwi da nauyinta ya kai kilo 5,344.1 a Jihar Lagos.

Alfijir Labarai ta rawaito hukumar ta fara kamen ne a kan hanyar Epe zuwa Lekki inda daga bisani jami’an hukumar da ke aiki a cikin teku suka yi kame a Alpha Beach da ke Jihar Legas.

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da NDLEA ta fitar a ranar Lahadi.

Ta bayyana cewa bayan samun bayanan sirri, jami’anta sun yi kwanton bauna a kan hanyar Epe zuwa Lekki da safiyar Litinin inda suka tare wata babbar mota dauke da wasu manyan buhunhunan  wiwi da nauyinsu ya kai kilo 2,434.1 a cikin motar.

Ba tare da bata lokaci ba direban motar ya yi tsalle ya fito daga motar inda ya gudu a cikin wata mota kirar hilux wadda ke yi wa motar wiwin rakiya.

Hakazalika sanarwar ta ce a kamen na biyu, jami’anta da ke aiki a cikin teku ne suka yi shi, bayan sumun  bayanan sirri, inda suka kama wani jirgin ruwa dauke da tabar wiwin da nauyinta ya kai kilo 2,910 a kusa da bakin ruwan Alpha kafin wanda ya fito daga Ghana.

Hukumar ta ce an kama wasu ‘yan kasar Ghana da suka hada da Monday Saba mai shekara 30 da kuma Hakeem Kwana mai shekara 27.

A Jihar Edo da ke kudancin Nijeriya kuwa,

Sanarwar ta ce jami’an nata sun far wa dajin Ekudo da ke Karamar Hukumar Uhunmwode a jihar Edo, inda suka lalata sama da kadada biyu ta tabar wiwi.

Hukumar ta ce bayan lalata gonar ta wiwin, sai da ta gano kilo 67 na tabar.

Ta kara da cewar, ta kama mutum shida bisa zarginsu da hannu a noman wiwin wadanda suka hada da Onyeka Onyedinma da Monday Onyedi da Alex Eboh da Edosa Imariagbe da Godbless Tunde da kuma Godstime Osarobo.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *