NDLEA Ta Kama Miyagun Kwayoyi 13,125kg, Da Mutane 793

Alfijr ta rawaito hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta kama kilo 13,125 na miyagun kwayoyi tare da cafke mutane 793 a babban birnin tarayya Abuja.

Kwamandan NDLEA na babban birnin tarayya Abuja, Kabir Tsakuwa ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai gabanin taron wayar da wayar da kan jama’a kan illolin miyagun kwayoyi a Abuja ranar Talata.

Tsakuwa ya ce 2022 shekara ce mai albarka ga rundunar, in da ya kara da cewa bayanan kamawa da yanke hukunci na da ban sha’awa.

Ya kara da cewa, shirye-shiryen na ba da shawara da gyaran hukumar, sun kuma samar da sakamako mai kyau a yankin.

A cewarsa, an kama mutane 793 da suka hada da maza 768 da mata 29, kuma hukuncin 167 ya kunshi maza 161 da mata shida.

Ya ce, “An kama kilogiram 13,125 na kayan maye daban-daban, sannan fasa-kwaurin magungunan da aka kama sun kai kilogiram 12,660.3 na tabar wiwi sativa.

“Sauran sun hada da kilogiram 21.957 na hodar iblis, kilogiram 0.008 da kilogiram 443.693 na sinadarai daban-daban na psychotropic, mutane 78 da suka hada da maza 74 da mata 4 da ke fama da matsalar shan miyagun kwayoyi, an samu nasarar yi musu nasiha tare da gyara su cikin lokaci guda”.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *