NDLEA Ta Kama Tabar Wiwi Mai Nauyin Kilogiram 476 A Kano

Alfijr

Alfijr ta rawaito hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama wani mutum mai shekaru 34 dauke da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 476 a Kano, inda ta kama allunan Tramadol 4,000 a Kano, Adamawa

Alfijr

Femi Babafemi, Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na NDLEA ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Sanarwar ta kara da cewa an kama wanda ake zargin Nasiru Abdulrahman a Kwanar Dan Gora, karamar hukumar Kiru ta jihar a ranar Juma’ar da ta gabata.

Alfijr

A cewar sanarwar, jami’an hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi sun kuma kwace allunan Tramadol 225mg guda 4,000 daga hannun wani matashi mai suna Abdulmiminu Abubakar mai shekaru 24 da aka kama a Gidan Madara dake karamar hukumar Mubi ta Arewa a jihar Adamawa.

Sanarwar ta kara da cewa an kama wanda ake zargin ne a lokacin da yake tafiya a kan babur domin kai maganin a garin Bukula na Jamhuriyar Kamaru.

Alfijr

“Ya yi ikirarin cewa wani wanda ake zargin Fahad Mohammed mai shekaru 19 ne ya ba shi kayan.

Daga baya an kama Fahad a wani samame da aka kai masa a gidansa da ke Unguwar Kasuwan Borkono a garin Mubi,” inji shi.

Alfijr

Shugaban Hukumar NDLEA, Brig. Janar Mohamed Buba Marwa (rtd) a cikin sanarwar yayin da yake yabawa jami’ai da mutanen jihohin Kano da Adamawa bisa namijin kokarin da suje, da sauran takwarorinsu na fadin kasar nan da su kara kaimi wajen yaki da duk wasu masu safarar miyagun kwayoyi a kowane bangare na Najeriya. .

Slide Up
x