NDLEA Ta Magantu Kan Cewar Dalibai 6 Cikin 10 Suna Amfani Da Miyagun Kwayoyi A Kano

FB IMG 1705321444130

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a jihar Kano ta yi karin haske kan wani rahoto da ke cewa dalibai shida cikin 10 da ke jihar suna shan kwayoyi…

Alfijir labarai ta rawaito Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a jihar Kano ta yi karin haske kan wani rahoto da ta fitar na cewa dalibai shida cikin 10 da ke jihar suna shan miyagun kwayoyi.

Sufeto na rundunar Jibril Ibrahim, ya bayyana cewa bisa ga bukata, adadin masu shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin dalibai ya yi yawa kuma za a iya cewa ya haura kashi 50 cikin 100.

Sai dai da yake karin haske kan rahoton, kakakin rundunar, Sadiq Muhammad Maigatari, ya ce alkaluman sun kebanta da abokan huldar da aka yi musu magani a cibiyar gyaran su.

Ya ce, “Abin da muka sani ya zo mana cewa alkaluman da wani ma’aikacinmu ya yi kwanan nan game da shan miyagun kwayoyi a tsakanin dalibai kuskure ne, kuma muna so mu tabbatar an bayar da sahihan bayanai ga jama’a.

“Kididdigan da aka yi a baya da ke nuna cewa a cikin kowane dalibai 10, biyar zuwa shida masu shaye-shayen kwayoyi ne, ya kebanta da abokan huldar da aka yi musu magani a cibiyar mu. Muna ba da hakuri ga duk wani rudani da wannan mummunar fassarar ta haifar.

Yana da kyau a lura cewa waɗannan alkaluma sun nuna yaɗuwar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ne kawai a tsakanin daidaikun mutane da ke neman magani a cikin cibiyarmu ba ta kowace hanya da aka shafi dukkan ɗaliban da ke karatu a Kano ba.

“Mun fahimci mahimmancin ingantattun bayanai a cikin maganganun jama’a, musamman idan ya zo ga batutuwa masu mahimmanci kamar amfani da miyagun ƙwayoyi.

Daily Trust

Don haka, muna ganin alhakinmu ne mu gyara duk wani rashin fahimta da kuma tabbatar da cewa an yada sahihin bayanai.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *