NDLEA Ta Sanar Da Ranar Fara Jarabawar Gwaji Ta Yanar Gizo Ga Masu Neman Aiki

Alfijr ta rawaito Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta sanar da yin jarabawar gwajin ta yanar gizo ga duk masu neman cancantar da suka yi nasarar gabatar da aikace-aikacen su na neman babban jami’in kula da aikinsu na Sufuritanda don aikin daukar ma’aikata na 2023.

Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a wata sanarwa ga manema labarai.

Ya kara da cewa duk masu neman aikin za su iya shiga dandalin tantancewarsu, wanda za a bude daga karfe 10:00 na safe ranar Litinin, 8 ga watan Mayu, har zuwa karfe 23:59 na yammacin ranar Laraba, 10 ga watan Mayu, 2023.

Babafemi ya ce, “Aikin tantancewar shi ne na farko a jerin gwaje-gwajen tantancewa da za a yi wa ’yan takarar da suka cancanta, wadanda za a tuntube su, ta hanyar Imel da suka mika tare da cikakkun bayanai kan yadda za a yi gwajin jarabawar tantancewar ta yanar gizo.

Ya kara da cewa, duk wanda ya cancanta ya duba akwatin saƙon imel ko spam daga ranar Laraba, 3 ga watan Mayu, don sanarwa da kuma umarnin yadda za su shiga jarabawar gwajin tantancewar ta yanar gizo.

Ya kuma bayyana cewa, ana sa ran duk masu neman aikin da suka cancanta za su zana jarabawar ta yanar gizo tsakanin lokutan da aka ambata a sama, kuma za a ba da karin umarni kan yadda za a shiga aikin tantance jarabawar gwajin.

Hakan ya faru ne yayin da ya bukaci dukkan masu neman shiga da su kammala jarabawar a cikin lokacin da aka ba su sannan su mika shi bayan sun bi umarnin da ke kan allon dan takarar a hankali.

“Za a bayar da karin umarni kan yadda za a shiga aikin tantancewar jarabawar gwajin a dandalin gwajin da kuma yayin wani bugu na musamman da hukumar ta NDLEA za tayi a shafinta na Twitter, wanda zai gudana a ranar Juma’a 5 ga watan Mayu tsakanin karfe 3 na rana zuwa 5 na yamma.

Haka kuma dukkan aikace-aikacen hukumar za’a same su ta shafin Twitter yana yawo kai tsaye akan asusun Facebook, YouTube, da Instagram.” in ji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

2 Replies to “NDLEA Ta Sanar Da Ranar Fara Jarabawar Gwaji Ta Yanar Gizo Ga Masu Neman Aiki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *