NDLEA ta tarwatsa wani gasar shan kwayoyi a gidan biki tare da kama Ango  

IMG 20231210 202322

Hukumar NDLEA ta tarwatsa wani bikin daurin aure a Katsina inda aka gudanar da gasar shan miyagun kwayoyi a wata unguwa Shola Quarters, an kama matasa 25 da suka halarci gasar.

Alfijir labarai ta rawaito mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi shi ne ya bayyana hakan ranar lahadi a Abuja.

Femi, yace mahalarta taron suna bi da bi ne wajen shan miyagun kwayoyi da aka jika a cikin bokitin roba a lokacin da jami’an suka kai sumame.

Ya kara da cewa an kama mutane uku da ake zargi da suka hadar da Monday John mai shekaru 50,sai Maryam Adang mai shekaru 48, da Mohammed Musa mai shekaru 36, a sassa daban-daban na jihar Kaduna a tsakanin ranar 7 zuwa 9 ga watan Disamba.

Ya kara da cewa an kama Adamu Nuhu mai shekaru 20 a ranar Litinin, 3 ga watan Disamba a kan hanyar Okene zuwa Lokoja zuwa Abuja yayin da yake dawowa daga Onitsha ya nufi Kaduna.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *