NJC ta yi wa wasu alƙalai ritayar dole bisa ƙaryar shekarun haihuwa

FB IMG 1751054448435

Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Ƙasa (NJC) ta amince da ritayar dole ga alkalai goma a jihar Imo.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, hukumar ta ce alkalai tara daga cikin su sun sauya shekarun haihuwarsu a cikin takardun aiki, yayin da alkali na goma, Theophilus Nzeukwu, aka kama da laifin yarda a naɗa shi a matsayin mukaddashin shugaban kotun jihar Imo ba bisa ka’ida ba.

Sanarwar ta ce:
“An gano cewa alkalai tara (9) daga cikin waɗanda abin ya shafa a bangaren shari’a na jihar Imo sun sauya shekarun haihuwarsu a cikin takardunsu na hukuma domin samun damar ci gaba da zama a kan kujerarsu fiye da lokacin da doka ta tanada.”

“Yayin da ɗayan alkalin, Mai Girma Alkali T. N. Nzeukwu, aka samu da laifin amincewa da naɗa shi a matsayin mukaddashin shugaban kotun koli ta jihar Imo duk da sanin cewa shi ne na hudu a jerin manyan alkalai na jihar, kuma hakan ya sabawa sashi na 271 (4) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya da aka yi wa gyara.”

Alkalai da lamarin ya shafa sun haɗa da:

M. E. Nwagboso (Babban Kotun Jihar Imo)

B. C. Iheka (Babban Kotun Jihar Imo)

K. A. Leaweanya (Babban Kotun Jihar Imo)

Okereke Chinyere Ngozi (Babban Kotun Jihar Imo)

Innocent Chidi Ibeawuchi (Babban Kotun Jihar Imo)

Tennyson Nze (Kotun Daukaka Kara ta Al’ada)

Ofoha Uchenna (Kotun Daukaka Kara ta Al’ada)

Everyman Eleanya (Kotun Daukaka Kara ta Al’ada)

Rosemond Ibe (Kotun Daukaka Kara ta Al’ada)

Hukumar NJC ta sake jaddada umarninta ga Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, inda ta bukace shi da ya naɗa mafi girman alkali a matsayin mukaddashin shugaban kotun jihar.

A wani zama daban, NJC ta haramta wa Alkali Isaac J. Essien na Kotun Kwadago ta Ƙasa samun karin girma zuwa wata babbar kotu har na tsawon shekaru uku saboda rashin da’a.

For Advert Or Advice Call +2348032077835

For more information about Alfijir labarai/Alfijir news fallow here 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *