PVC! Kotu Ta Daure Wani Shugaban APC A Kano shekara 2, A Gidan Gyaran Hali

Alfijr ta rawaito Shugaban Jam’iyyar APC Na Yautar da ke karamar Hukumar Gabasawa ta Jihar Kano an yanke masa hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari bisa samunsa da laifin mallakar katin zabe na dindindin guda 367 mai suna daban-daban. Sabanin sashe na 22 (a) na dokar zabe, 2022 kamar yadda aka gyara.

Sai dai Alkalin Kotun Mai shari’a Faroukh Ibrahim Umar ya baiwa wanda aka yanke wa hukuncin zabin Naira 500,000. Dangane da laifin hada baki, sabanin sashi na 97 na dokar Penal Code, kotun ta yanke hukuncin daurin watanni 6 a gidan yari tare da zabin tarar N50,000.

Kotun ta yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin ne bayan ya amsa laifuka biyu da ake tuhumarsa da shi.

Kamar yadda rahoton farko ya nuna, (FIR) Aminu Ali ya kasance a ranar 10 ga Oktoba 2022 da misalin karfe 2100 na safe ya hada baki da wani Aminu Manga Zakirai na karamar hukumar Gabasawa Kano tare da karbar katin zabe.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *