Ramuwar Gayya! Harin Hamas Ya Raunata Mutane A Tel Aviv

FB IMG 1728310772528

Bayanan hoto,Yadda motoci suka tsaya a bisa babbar hanyar Ayalon a cikin birni Tel Aviv, inda mutane suka fito daga motocinsu domin yin ta kansu.

Dakarun tsaron Isra’ila sun ce an harba makamai masu linzami biyar daga yankin Khan Younis na Gaza zuwa Tel Aviv.

Hamas ta tabbatar da cewa ita ce ta kai harin.

Tawagar BBC ta ce ta jiyo ƙarar fashe-fashe, yayin da motoci suka cirko-cirko a kan babbar hanyar Ayalon.

Sashen bada agajin gaggawa na Isra’ila sun ce mata biyu matasa da makaman suka faɗawa sun jikkata a tsakiyar Isra’ila, an kuma garzaya da su asibiti.

Tunda farko dai, sojojin Isra’ila sun ce sun daƙile duk wata barazana ta Hamas, inda suka ce sun kakkaɓo makamai masu linzami uku da Hamas din ta harba.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *