A birnin Yamai, babbar ma’aikatar ’yan sanda DPJ ta bankado wasu gaggan gungun barayi guda hudu da suka yi karin suna wajen fashi da makami, kisan kai, danfara, sacen kaya, da rike bindiga ba tare da izni ba.
Alfijir labarai ta rawaito a kokarin da hukumomin birnin Yamai suke yi domin kawar da matsalar tsaro a babban birnin kasar.
Ofishin ’yan sanda na PJ dai a ranar Talata, ya gabatar da wasu gungun barayi guda hudu da suka shawara wajen fashi da makami, kuma dukkan su ’yan kasar Nijar ne, sun kuma jima suna addabar mazauna birnin Yamai kafin dubunsu ta cika.
Wadannan gungun barayi sun shahara wajen sata cikin dare, da amfani da makamai, da hada kai da wasu domin shiga cikin gidajen mutane, da kuma balle shaguna.
Rahotanni sun nuna cewar ta’asar da suka tafka ta baya bayan nan a cewar shugabannin ’yan sanda na DPJ ta faru ne a cikin daren 30 ga watan Nuwamba zuwa ranar 1 ga watan Disamban shekarar 2023, inda suka bude wuta kan wasu mutane guda hudu, Yan uwan juna ,daga cikinsu akwai mace guda mai juna biyu, tare da jikkata wasu daga cikinsu da kuma yin awon gaba da kudade jaka dari 6 na Sefa.
Bayan gudanar da bincike, an kama barayin, haka zalika binciken ya taimaka wajen kama kayayyaki daban daban da suka hada da bindigogi, adduna, sanduna, da kuma sauran kayayyakin da ake amfani da su domin gudanar da ayyukansu.

CRI Hausa
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp