Dubun wasu matasa uku da rundunar yan sandan jihar Kano ta kama da wayoyin hannu 318 wadanda ake zargin na sata ne ta cika.
Alfijir Labarai ta rawaito kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a shafin sada zumunta ranar Asabar.
Kiyawa ya bayyana cewa tun da farko wani mai suna Muhammad Adam da wasu mutane 9 ne suka kai musu korafi kan cewa da tsakar dare barayi sun fasa musu shaguna a kusa da filin wasa na Sani Abacha dake kofar Mata Kano, inda suka sace wayoyi 671.
Nan take ‘yan sanda suka soma bincike wanda har ya kai ga kama mutanen uku, sun kuma amsa laifin da ake zargin su da aikata wa.
Sai dai wadanda ake zargin sun shaida wa ‘yan sandan cewa tuni suka sayar da wasu daga cikin wayoyin.
SP ya bayyana cewa za a gurfanar da mutunen a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo