‘Yan kasar Nijar sun kwashe wata da watanni suna gudanar da zanga-zangar kyamar Faransa da neman ta kwashe dakarunta daga kasar
Alfijir Labarai ta rawaito Rundunar sojin Faransa ta bayyana cewa za ta soma kwashe dakarunta daga Jamhuriyar Nijar a wannan makon bayan dangantaka ta yi tsami tsakanin kasashen biyu sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yuli.
“Za mu soma kwashe dakarunmu a wannan mako, a cikin tsari, tare da hadin gwiwar ‘yan kasar Nijar,” a cewar sanarwar da hedikwatar rundunar sojin ta fitar ranar Alhamis.
Ranar 24 ga watan Satumba Shugaba Emmanuel Macron ya ce Faransa za ta kwashe dukkan dakarunta 1,400 da jakadanta da ke Nijar nan da karshen shekarar 2023
Ranar Talatar da ta wuce Jakada Sylvain Itte ya fice daga kasar wata guda bayan sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum sun ba shi wa’adin awa 48 ya bar kasar bayan “ya ki amsa gayyatar ma’aikatar harkokin waje don halartar taron” da aka gayyace shi da kuma “wasu matakai da Faransa ta dauka da suka ci karo da muradan Nijar”.
Faransa ta jibge dakarunta a Nijar ne domin yaki da kungiyoyin ‘yan ta’adda masu alaka da Al Qaeda da Islamic State da suka addabi yankin Sahel.
Kasar ta aika sojojinta kusan 400 su yi aiki da sojojin Nijar a kan iyakar kasar da Burkina Faso da Mali don murkushe masu tayar da kayar baya.
Hedikwatar sojin Faransa ta ce sojojinta suna bukatar tsaro, ciki har da kariya ta sama, kafin su fita daga sansaninsu don ficewa daga Yamai, babban birnin Nijar.
Dakarun Faransa sun fada cikin halin rashin tabbas tun bayan da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar suka umarci su fice daga kasar, inda ba sa samun isasshen abinci sannan dubban ‘yan Nijar sun yi wa sansaninsu tsinke suna neman su fita daga kasar.
Dakarun na Faransa suna da zabi biyu ne na fita daga Nijar – ko dai ta kasar Benin — ko kuma ta Chadi saboda Nijar ta haramta wa jiragen Faransa shiga sararin samaniyar kasar.
Faransa ta kara yawan dakarunta a Nijar bayan sojojin da suka yi juyin mulki a Mali sun kore ta daga can, inda ta aika karin jiragen helikwafta da jirage marasa matuka da jiragen yaki.
TRT Afrika da abokan hulda
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb