Daga Aminu Bala Madobi
A wani yunkuri tun bayan darewa kujerar mulki, Shugaban Ghana ya fara wani shiri na maido da kasashen da suka balle daga kungiyar ECOWAS.
John Dramani Mahamma ya fara da yada zango a birnin Bamako na kasar Mali kafin daga bisani ya je birnin Yamai da Ouagadougou kamar yadda rahotanni suka nuna.
Rahotonni sun ce makasudin ziyarar shugaba Mahamma a kasashen uku na kungiyar AES shine na kara lallabar kasashen domin su dawo kungiyar ECOWAS wacce suka fice daga cikin ta
A ziyarar sa ta baya bayan nan a kasar Côté d’ivoire an jiyo shugaba John Dramani a gaban takwaransa Alassan Ouattara yana cewa tafiyar 15 tafi ta 3 wanda hakan ke nuna cewa sarkin yawa yafi sarkin karfi
Bayanai sunce bayan kammala tattunawa da Shugabannin, ana saran jin cikakken rahotanni daga kungiyar kasashen Sahel wadda ta jaddada matsayar ta na kin komawa ECOWAS.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ