San Kano Ya Gudanar Da Gagarumin Hawan Daba A Birnin Kano

Alfijr ta rawaito martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero (CFR) yayi hawan Daba a ranar Lahadin da ta gabata domin godewa Allah abisa lambar yabo ta CFR da shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari ya bashi a kwanakin baya.

Wannan kasaitacciyar Dabar ta samin halartar yawancin al’ummar kano hadi da sassa daban daban na kasar nan, da makwaftan kasar.

Mai girma Mataimakin Gwamnan Jihar Kano yana ďaya daga cikin manyan mutane da suka halarci wannan Dabar da ta gudana a Fadar Mai martaba Sarkin Kano da ke kofar kudu.

Hawan daba dai wani hawa ne akasari da fadar kano ke gudanar dashi domin karrama wasu baki da aka yi daga kasashen duniya ko kuma wani bikin da masarauta ke gudanarwa don murnar wani al amarin.

Muna daga nan jaridar Alfijr Labarai muna taya mai martaba murnar wannan karamci da shugaba Buhari ya yi masa tare da dan uwansa Sarkin Bichi.

Allah ya jikan Takawa ya jikan mai babban Daki, aljanna makoma

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *