Sanata Barau Ya Gana Da Ƴan Majalisa 70 Kan Takarar Shugabancin Majalisar Dattawa

Alfijr ta rawaito Daya daga cikin masu neman kujerar shugaban majalisar dattawa Sanata Jibrin Barau na jam’iyyar All Progressives Congress ya karbi bakuncin zababbun sanatoci sama da 70 domin neman goyon bayansu gabanin kaddamar da majalisa ta 10 da za ta kafa shugabancin babban zauren majalisar.

Barau, wanda shi ne karo na uku a zauren majalisar da ke wakiltar Kano ta Arewa a majalisar dattawa.

Duk da cewa har yanzu bai fito fili ya bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar kujerar da ake nema ba, ya tura wakilansa domin ganawa da manyan masu ruwa da tsaki ciki har da manyan ‘yan majalisar tarayya.

A halin yanzu yana shugabantar kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa.

An tattaro cewa zababbun sanatoci sama da 70 ne suka halarci liyafar cin abincin rana da aka yi a otal din NICON da ke Abuja ranar Talata.

An gudanar da taron ne bayan gabatar da takardar shaidar cin zabe ga ‘yan majalisar.

A ranar Talata ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga akalla zababbun Sanatoci 98 a dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja ranar Talata.

Jam’iyyun siyasa bakwai ne suka lashe kujerun majalisar dattawa, inda APC ta samu rinjaye da kujeru 57.

Jam’iyyar Peoples Democratic Party ta lashe kujeru 29; Jam’iyyar Labour shida; Sabuwar Jam’iyyar Jama’ar Najeriya, biyu; Social Democratic Party, biyu; jam’iyyar All Progressives Grand Alliance da Youth Peoples Party, daya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *