Daga Aminu Bala Madobi
Bayanai sun nuna akwai alamun za a kirkiro sabuwar jiha nan ba da jimawa, biyo bayan gabatar da kudirin kafa jihar Tiga daga Kano a majalisar dattawan Najeriya.
Kudurin dokar wanda Sanatan Kano ta kudu Suleiman Abdurrahman Kawu Sumaila ya gabatar, wanda tuni aka yi masa karatu na farko a ranar laraba 10 ga Yuli, 2024.
Kudirin doka mai taken “Constitution of the Federal Republic of Nigeria, 1999 (Alteration) Creation of Tiga State Bill, 2024 (SB.523)” na da nufin raba jihar Kano zuwa jihohi biyu, inda Tiga za ta zama sabuwar jihar da za a kirkire ta daga jihar kano.
Alfijir labarai ta ruwaito a zaman majalisar da aka gudanar a yau, Kawu sumaila ya ce kirkiro da sabuwar jihar daga kano mai kananan hukumomi 16 abune muhimmi da zai inganta tattalin arziki da cigaban jamaa.
Kudirin ya sami karbuwa matuka kasancewar tuni takwaran sa Hon. Kabir rurum, mai wakiltar Rano Kibiya Bunkure ya gabatar da makamancin wannan kudiri a zauren majalisar wakilai, kuma ya sami goyon bayan yan uwa yan majalisu da dama.
Dan majalisar dattawan yace ya zama wajibi a sami amincewar zauren ‘yan doka, yan majalisar wakilai kafin a kaiga amincewa.
Sumaila ya jaddada cewa yana yakini kudirin zai wuce dazarar an dawo zaman majalisar na gaba.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne Majalisar Dattawa ta karbi kudirin kafa Jihar Anioma a yankin Kudu maso Gabas, wanda Sanata Ned Nwoko daga Delta ta Arewa ya gabatar.
Bugu da kari, an gabatar da kudirin dokar kafa jihar Orlu, wanda Sanata Osita Izunaso da mai wakiltar Ikenga Ugochineyere, da kuma jihar Etiti suka gabatar, wanda dan majalisa Amobi Godwin Ogah da wasu ‘yan majalisa hudu daga al’ummomin da abin ya shafa suka dauki nauyinsa.
Akwai kuma kiraye-kirayen a kirkiro sabbin jihohi daga Legas da sauran sassan kasar nan.
Wanne gari kuke ganin zai fi da cewa ya zama babban birni (Wato State Capital)???
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj