Shettima Ya Zargi Shugaba Tinubu da Saka Na’urorin Leken Asiri a Gidan Hukuma na Biliyan 21.

IMG 20250302 WA0003

Daga Aminu Bala Madobi

Watanni takwas bayan kaddamar da shi, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya ƙi komawa gidansa na hukuma da aka gina don Mataimakin Shugaban Ƙasa, inda rahotonni ke nuna irin zargin cewa an saka na’urorin sadarwa da tsaro a cikin gidan na biliyan 21.

Bayanai sun ce na’urorin leƙen asirin an girka su don sa ido kan irin ayyukan da zai rika gabatar wa a gidan.

Wani makusanci ga Mataimakin Shugaban Ƙasa ya nuna cewa, saboda rashin jituwa dake tsakanin shugabannin arewa game da wa’adin mulki na biyu na Shugaba Bola Tinubu a 2027, Mataimakin Shugaban Ƙasa ya san cewa ana sa ido da lissafi kan ayyukansa daga Shugaba Tinubu da amintattunsa.

Haka nan, rahotonni sun nuna cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa ya ji labarin yunkurin maye gurbinsa a 2027 da Yakubu Dogara a matsayin wanda ake yayatawa don maye gurbinsa, don haka yana ganin komawa gidan hukuma na Mataimakin Shugaban Ƙasa ɓata lokaci ne.

Majiyar ta ce, Mataimakin Shugaban Ƙasa yana sane da wannan zargin, yana jin cewa komawa sabon gidan zai sauƙaƙa sa ido kan dukkan motsinsa da kula da irin baƙin da yake karɓa a gidansa da ofishinsa da irin tattaunawar da ake yi a cikin ginin.

A watan Yuni 2023, wata guda bayan rantsar da Shugaba Tinubu da Shettima, gwamnati ta kaddamar da gidan Mataimakin Shugaban Ƙasa, wanda ya kashe naira biliyan 21 wajen gina shi.

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa an ba da aikin a farashin naira biliyan 7 a 2010 amma aka yi watsi da shi bayan wasu gyare-gyare na farko.

Shugaba Tinubu ya kaddamar da gidan naira biliyan 21 na Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima a ranar 7 ga Yuni, 2024.

Shugaban ya bayyana cewa samar da madaidaicin matsuguni ga Mataimakin Shugaban Ƙasa ba kawai batun jin daɗi ba ne, face alamar girmamawa ga ofishin da mutanen da ke riƙe da shi.

✍️ Tushen labari. Jackson Ude.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *