Shin Ko Kun San Masu Shirin Jagorantar Zanga-zanga A Najeriya? To Sun Bayyana Kansu

B7

Wasu ƙungiyoyi da ke shirin jagorantar zanga-zanga a Najeriya, sun fito sun bayyana kansu a wani taro da suka gudanar a jihar Kano a ranar Talata.

Gamayyar ƙungiyoyin daga arewacin Najeriya sun jaddada cewa ba gudu ba ja da baya za su fito zanga-zangar da suka ce za su jagoranta a sassan arewacin kasar, duk da gargaɗi da roƙon gwamnati su ƙara haƙuri su jingine zanga-zangar.

Ƙungiyoyin sun shirya gudanar da zanga-zangar ta kwana 10 daga ranar Alhamis 1 ga Agusta.

Sun ce zanga-zanga ita ce kawai zaɓin da ya rage masu domin nuna fushinsu kan halin da Najeriya ke ciki na matsalolin tattalin arziki da tsaro.

Amma hukumomin gwamnati na ci gaba da gargaɗin yiyuwar tashin hankali kuma wasu na iya amfani da zanga-zangar su wawushe dukiyoyin al’umma.

Farashin kayan masarufi a Najeriya sun yitashin gauron zabi da ba a taɓa gani ba a tarihi, ɗaya daga cikin dalilin da ke ingiza zanga-zangar da ta ja hankali a shafukan sada zumunta.

Masu shirin jagorantar zanga-zangar kuma yanzu sun fito sun faɗi dalilansu da kuma buƙatu da yadda suka tsara gudanar da zanga-zangar.

Waɗanne ƙungiyoyi ne?

Wata gamayyar ƙungiyoyi ƙarƙashin inuwar kungiyar tabbatar da kishin kasa ta NPFM ta fito ta bayyana kanta da cewa ita ce za ta jagoranci zanga-zanga a arewacin Najeriya.

Bayan taron da suka gudanar a jihar Kano a ranar Talata, ƙungiyoyi 13 na arewacin Najeriya sun jaddada aniyarsu ta jagorantar zanga-zangar, a cikin wata sanarwa da suka fitar.

Sun ce ba gudu ba ja da baya za su fito zanga-zanga kamar yadda suka tsara gudanarwa daga ranar Alhamis 1 ga Agusta a sassan arewacin Najeriya.

Masu jagorantar zanga-zangar sun bayyana sunayensu tare da gabatar da buƙatu da umarni na matakan da suka ɗauka daga ranar 1 ga watan Agusta da za su soma zanga-zangar.

Sun ce zanga-zangar da za su yi ta lumana ce kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba su dama.

Daga cikin bukatun zanga-zangar da suka zayyana sun haɗa da tilasta wa gwamnati rage farashin litar man fetur tsakanin N160 zuwa N200 da rage farashin kayan abinci da lantarki da kudin ruwa da kuma rage kudaden da ake kashewa wajen tafiyar da gwamnati tare da kawo ƙarshen matsalolin tsaro a Najeriya.

Sannan masu shirya zanga-zangar sun tsara umarni ga waɗanda za su shiga zanga-zangar.

“Babu buƙatar wani ya ɗauki makami, kuma kada wanda ya nemi ya ci zarafin wani ko yunƙurin tayar da hankali,” kamar yadda suka bayyana cikin sanarwar da suka fitar

Sannan a cikin umarnin sun haramta wawushe dukiyar mutane.

Kungiyoyin sun kuma fadi lokaci da wuraren da za su hadu domin zanga-zangar.

Daga kudancin Najeriya akwai ƙungiyar “Take It Back movement” da ta fito ta bayyana cewa tana cikin masu shirya zanga-zangar.

Jagoran ƙungiyar Banwo Olagokun ya ce zanga-zangar ta zama dole.

“ZA mu yi zanga-zanga ne saboda yunwa, hauhawar farashi ta sa ba mu iya samun manyan buƙatu na rayuwa – abinci da ruwa da magani,” in ji shi.

Zanga-zangar dai ta ja hankalin gwamnati, inda ta tilasta wa shugaban ƙasa jagorantar tarukan gaggawa, yayin da jami’an tsaro ke gargaɗi na ɗaukar matakai domin kauce wa jefa ƙasar cikin tashin hankali.

Yunwa na ɗaya daga cikin babban dalilin da ya jefa ƴan Najeriya cikin ƙunci da rashin jin daɗi kuma ita ce ke ingiza batun gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar.

Masu da’awar zanga-zangar na cewa, ita ce kawai mafita duk da cewa gwamnati ta ce tana jin kokensu tare da ci gaba da ɗaukar matakai na saita al’amurra tare da raba tallafi ga yan kasa musamman da ke cikin talauci da masu karamin karfi.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *