Shugaba Tinubu Ya Tumbuke Shugaban Hukumar Alhazai Jalal Arabi Ya Nada Wani

IMG 20240820 WA0008

Daga Aminu Bala Madobi

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sallami Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Malam Jalal Arabi.

Alfijir labarai ta ruwaito sallamar tasa na zuwa ne bayan zargin shugaban da yin sama da fadi da wani ɓangare na naira biliyan 90 da gwamnatin Najeriya ta ba hukumar a matsayin tallafi ga aikin hajjin 2024 da ya gabata.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Ajuri Ngelale ya fitar, ta kuma tabbatar da naɗa Farfesa Abdullahi Saleh Usman a matsayin sabon shugaban hukumar ta alhazan Najeriya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *