Shugaba Tinubu ya yi umarnin zartar da rahoton da zai rage da haɗe ma’aikatu a Najeriya

IMG 20240224 WA0173

Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin aiwatar da cikakken rahoton Oronsaye wanda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kafa tun a 2011, a kokarin gwamnati na rage yawan kashe kudaden gudanarwa.

Alfijir labarai ta rawaito an dai kafa kwamitin ne a lokacin sake fasalin tsarin mulki da kwamitoci da hukumomin gwamnatin tarayya karkashin shugabancin tsohon shugaban ma’aikata na Najeriya, Stephen Osagiede Oronsaye.

Kwamitin ya gabatar da rahoto mai shafuka 800 a ranar 16 ga Afrilu, 2012, inda ya bankado yadda ake gudanar da gasa a tsakanin hukumomi da dama, wanda ba wai kawai ya haifar da rashin kwanciyar haknali a tsakanin hukumomin gwamnati ba, har ma ya haifar da almubazzaranci.

Rahoton ya ba da shawarar dakatar da tallafin da gwamnati ke bai wa wasu hukumomi da majalisu wajen bayar da kuɗi don gudanar da manyan ayyuka.

Rahoton na Oronsaye ya tabbatar da cewa akwai ma’aikatun gwamnatin tarayya 541 da kwamitoci da hukumomi (na doka da na shari’a), inda ya bayar da shawarar cewa a mayar da 263 daga cikin ma’aikatun zuwa 161, yayin da rahoton ya ce a soke hukumomi 38 sannan a hade guda 52.

Kwamitin ya kuma ba da shawarar cewa 14 daga cikin hukumomi su koma sassan ma’aikatu.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, da yake jawabi ga manema labarai a fadar shugaban ƙasa a ranar Litinin a Aso Rock, Abuja, ya ce “a cikin wani gagarumin yunkuri a yau, gwamnatin shugaban Tinubu ta dauki matakin aiwatar da rahoton da ake kira Oronsaye Report don amfanin Najeriya”

“Yanzu, abin da hakan ke nufi shi ne, an soke wasu hukumomi da kwamitoci, da wasu sassa a zahiri. Wasu kuma an gyara su, kuma an yi musu alama yayin da wasu kuma an rage su. Wasu kuma, ba shakka, an dauke su daga wasu ma’aikatun zuwa wasu inda gwamnati ke ganin za su yi aiki sosai.”

Da take tsokaci kan wannan lamari, mai bai wa shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin siyasa Hadiza Bala Usman, ta ce hakan ya yi daidai da buƙatar rage yawan kudaden gudanar da harkokin mulki da kuma daidaita yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati.

Ta kara da cewa an kafa tawaga don aiwatar da rahoton cikin makonni 12.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *