Shugaban Jam’iyyar Apc  Na Kano Yayi Martani Ga Shugaban NNPP Na Kano

FB IMG 1720449129873

Jam’iyyar All Progressives Congress APC ta ce jam’iyyar New Nigeria Peoples Party NNPP za ta sha kaye a zabe a 2027,  saboda son zuciyar da ta ke yi na rikicin masarautar Kano.

Alfijir labarai ta ruwaito Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Abdullahi Abbas, a wata sanarwa da ya fitar yau Litinin a Abuja, ya ce maimakon batun da ya shafi damar zaben shugaban kasa Bola Tinubu, maimakon haka NNPP za ta fuskanci illa.

Ganin cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba shi da Daraja a matakin kasa na zama shugaban Najeriya, APC ta ce yanzu ta fi da hadin kai da farin jini  kuma za ta kai gaci ga rubi uku na abin da ta samu a zaben shugaban kasa da ya gabata a jihar Kano sakamakon gazawar da aka yi a halin gudanarwa a jihar.

Jigon na APC ya ce sabanin rahoton da kafafen yada labarai suka bayar ga shugaban NNPP na jihar Kano, Hashimu Dungurawa da jam’iyyar da ke mulki a jihar da kuma shugabanta na kasa, Kwankwaso za su fuskanci mummunan rikicin Sakamakon barkewar rikicin masarautar.

Shugaban NNPP na Kano ya ce rikicin sarautar na iya yin illa ga burin Shugaba Bola Tinubu a wa’adi na biyu a 2027.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *