Shugaban Najeriya Ya Bada Umarnin Hana Shigo da Kayayyakin Amurka cikin Najeriya

FB IMG 1754600090124

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya bayyana rashin jin daɗinsa da damuwa kan matakin da gwamnatin Najeriya ta ɗauka na haramta shigowa da wasu kayayyakin Amurka cikin Najeriya a matsayin martani ga harajin kashi 14 cikin ɗari (14%) da gwamnatin Amurka ta kakaba kan kayayyakin da ake shigowa da su daga Najeriya.

Sai dai wasu na ganin matakin da Tinubu ya dauka na da alaka da barazanar da Trump yayi na fara kaiwa Najeriya hari saboda zargin yawan Kashe kiristocin kasar.

Rahotanni daga ma’aikatar kasuwanci ta Amurka sun bayyana cewa wannan sabani tsakanin ƙasashen biyu na iya janyo koma baya a dangantakar kasuwanci da tattalin arzikin da Najeriya da Amurka suka gina tsawon shekaru.

Wata majiya ta ce kayayyakin da abin ya fi shafa sun haɗa da kayayyakin fasaha,da kayan abinci, da wasu kayayyakin masana’antu da ake shigowa da su daga Amurka zuwa Najeriya.

Masana harkokin tattalin arziki sun yi gargadin cewa matakan da ɓangarorin biyu suka ɗauka na iya ƙara tsada ga kayayyaki a kasuwannin cikin gida, tare da rage jarin da kamfanonin waje ke zubawa a Najeriya.

Hakazalika, akwai yiwuwar hakan ya shafi kasuwancin man fetur da wasu kayayyakin noma da Najeriya ke fitarwa zuwa ƙasashen waje.

Gwamnatin Najeriya ta ce matakin nata ba don yin gaba da Amurka ba ne, sai dai domin kare muradun tattalin arzikinta da masana’antunta na cikin gida.

Sai dai, a nata ɓangaren, gwamnatin Amurka ta bukaci Najeriya da ta sake duba matakin, tana mai cewa hakan na iya kawo cikas ga yarjejeniyoyin cinikayya da suke tsakanin ƙasashen biyu.

Rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin hukumomin kasuwanci na ƙasashen biyu domin warware sabanin cikin lumana, yayin da masana ke kira da a nemi mafita ta hanyar tattaunawa domin guje wa tabarbarewar huldar diflomasiyya.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *